<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Rayukan Duk Jama'a A Gabanka Su Ke LW319</title>
<lyrics>[V1]
 1) Rayukan duk jama'a a gabanka su ke,
 Mutanen dukan zamanu, kowace halitta. Harsunan dukan duniya, yamma da gabas kuwa,
 Gare ka su ke rerawa, Maɗaukaki ne kai.

[V2]
 2) Ga wanda mu ke ƙauna, Mai Cetonmu ne shi,
 Sunansa yana goshinmu, suna mai tsarki.
 Shi ne kaɗai da iko, mai kā da mutuwa,
 Yesu na Nazarat a dā, Allah har abada.

[V3]
 3) Mu ma a wannan duniya, a tsakiyar yaƙinmu,
 Mun karƃi iko wurinka, Yesu Shugabanmu.
 Mu dai mun ji kiranka, ba za mu fasa ba.
 Ƴan yaƙi nan, mu huta can, hutu madauwami.</lyrics>
<hymn_number>319</hymn_number>
</song>